Wannan manhajace ta karatun Ahalari da Malam yayi lokacin rayuwarsa
Karatun littafin Akhdari (Ahalary) da marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya gabatar lokacin ya raye (Allah Ya gafarta masa).
Littafin Ahalari Littafi n Fikihu ne da yake karantar da mutane Ibada akan Mazhabar Malikiyya a mataki na karami, wanda ya kunshi tun daga tsarki har zuwa Kabli da Ba'adi a cikin Sallah.
Malam Abubakar Mahmud Gumi, tsohon Alkalin Alkalai ne a yankin Arewacin Najeriya. Mai bayar da fatawa na Kasa, Mai Fassarar Alkur'ani mai girma a cikin harshen Hausa da Larabci.