Usar la aplicación APKPure
Obtener Complete Tafseer Sheikh Ja'afar Mahmud 2003 Part 1 versión histórica en Android
Serie completa Tafseer Sheik Jafar Mahmud Adam 2003 Parte 1
Complete Tafseer Sheikh Ja'afar Mahmud 2003 Part 1
Complete Tafseer Sheik Jafar Mahmud Adam 2003 series Part 1
***Tarihin Sheikh Jafar Mahmud Adam***
An haifi marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam a garin Daura, a shekara ta 1962 (ko da yake wani lokacin yakan ce 1964).
Marigayi Sheikh Ja'afar ya fara karatunsa na allo a gidansu, a wurin mijin yayarsa, Malam Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini.
Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari wai shi Koza, kimanin kilomita 9 a arewa da Daura, wanda shi ma akwai dangantaka ta jini a tsakanin su, wanda kuma shi ne musabbabin zuwansa Kano. Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a shekara ta 1971 (ko 1972), sai suka zauna a makarantar Malam Abdullahi, wanda asalinsa mutumin jamhuriyar Nijar ne, amma yake zaune a unguwar Fagge a Kano.
Tun kafin zuwansu Kano, tuni marigayi Sheikh Jaafar ya riga ya fara haddar Alkur'ani mai girma, wanda ya kammala a shekara ta 1978.
Bayan da Malam ya kammala haddar Alkur'ani mai girma, kasancewarsa mai sha'awar
ilimi, sai ya shiga makarantu biyu a lokaci daya a shekara ta 1980. Ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen kasar Misra a cibiyar yada al'adun kasar Misra, (Egyptian
Cultural Centre), sannan kuma ya shiga makarantar manya da ba su yi boko ba ta Masallaci Adult Evening Classes, tunda a lokacin shekarunsa sun wuce shekaru
na primary, amma duk da haka a wannan lokaci shi ne mafi kankanta a ajinsu. Haka ya rika yin wannan karatu guda biyu: Waccan makarantar ya je ta da daddare bayan sallar isha'i, waccan kuma ta koyo harshen larabcin da yamma. Ya kammala wadannan makarantu a shekara ta 1983. Wannan kuma shi ya ba shi damar shiga makarantar
GATC Gwale a shekara ta 1984, kuma ya kammala a shekara ta 1988.
A shekara ta 1989, malam jafar ya sami gurbin karatu a jami'ar musulunci ta Madinah, a inda ya karanta ilimin tafsiri da Ulumul Kur'an, wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993. Sannan kuma Sheikh Ja’afar ya sami damar kammala karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Musulunci, A Oundurman Sudan. Sannan kuma, kafin rasuwarsa, ya riga ya yi nisa wajen karatunsa na digiri na uku, wato digiri da digirgir (PhD), a Jami’ar Usman Dan Fodiyo da take Sokoto.
Daga cikin malamansa na ilimi, akwai:
- malaminsa na farko, mutumin kasar Masar, Sheikh Abdul-Aziz Ali al-Mustafa
- Malam Nuhu a unguwar Dandago, wanda malam ya karanci ilimi fikihun malikiyya da wadansu littattafai na hadisi a gurinsa
- Malam Muhammad Shehu, mutumin Lokoja, wanda Malam ya karanci nahawu da sarfu da balaga da adab a wajensa.
-Sheikh Abubakar Jibrin limamin masallacin Juma'a na BUK
- Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim shi ma na jami'ar Bayero ta Kano.
Daga cikin malaman mallam jafar na jami'a kuma akwai: Sheikh Abdurrafi'u da Dr. Khalid Assabt.
Daga cikin karatuttukan da malam ya karantar da su, sun hada da:
1. Karatun alkurani mai girma wato sheikh ja'afar mahmoud Holy Quran recitation
2. complete tafseer of the Holy Quran mp3 sheikh jafar Mahmud
3. Kitab tauhid
4. Umdatul Ahkaam
5. Arba'una Hadiith
6. Kashfusshubuhaat
7. Bulugul Maraam
8. Riyaadussalihiin
9. Siratun Nabawiy
10. Ahkaamul Janaa'iz
11. Siffatus Salaatun Nabi
Kafin rasuwarsa, malam ya fara gagarumin aikin rubuce tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin cibiyar (Sheikh Ja'afar Islamic Documentation Centre).
Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ya rasu ranar juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428 (13/04/2007) sakamakon harin da wadansu 'yan ta'adda suka kai masa, a daidai lokacin da yake jagorantar sallar asuba a masallacin Juma'a na Dorayi. Ya rasu ya bar mata biyu, da 'yaya shida, yayin da aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 daidai bayan aiwatar da wannan kisan gilla a kansa. Dubun-dubatar mutane ne daga ko'ina cikin kasar nan suka halarci jana'izarsa, kuma an binne shi ne a makabartar Dorayi.
Presentado por
Àziz Pàtron
Requisitos
Android 4.1+
Categoría
76.7 MB 11/10/2018
76.7 MB 11/10/2018
76.5 MB 05/06/2018
76.5 MB 05/06/2018
Usar la aplicación APKPure
Obtener Complete Tafseer Sheikh Ja'afar Mahmud 2003 Part 1 versión histórica en Android
Usar la aplicación APKPure
Obtener Complete Tafseer Sheikh Ja'afar Mahmud 2003 Part 1 versión histórica en Android