Tasirin Da Kuma Amfanin Biyayya Zuwaga Iyaye
Abdullahi RA yace Na tambayi Manzon Allah SAW cewa wane aikine Allah mai girma da daukaka yafi so sai yace Sallah akan lokacinta sai nann sannan me Sai yace Bin Iyaye sai nann sannan me Sai yace Sannan Jihadi don daukaka kalmar Allah. Sannan yace ya fada mun wainnan abubuwan kuma da naso ya karamun da ya karamin.
Abdullahi bin Umar RA yace Yardan Allah yana cikin yardan iyaye kuma fushin Allah yana cikin fushin iyaye Wato wanda iyayensa suka yarda dashi to Allah zai yarda shi haka ma idan iyayensa suna fushi dashi to Allah ma yana fushi dashi.
A wani hadisin kuma Abdullahi dan Abbas yace Lallai ni ban san wani aiki wanda yafi kusanci zuwa ga Allah ba fiye da biyayya
ga Mahaifiya Duka hadisan suna cikin Al-Adabul Mufrad.
Allah kasa mu kasance masu farantama Iyayen mu