Nagartattun addu’o’i daga bakin manzon tsira Annabi Muhammadu (SAW) da Al Qur'an
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbatar a gare shi ya kasance yana yawan ambaton Allah da tunawa da Shi a koda yaushe, kuma a duk halin daya samu kansa ciki.
Haka zalika yana koyar da sahabbansa yadda zasu dinga ambaton Allah da kasancewa cikin shaukin
tunaninsa. Mun dan tsakuro muku kadan daga cikin addu’o’in da Annabi ya kanyi a lokutta daban daban.
1-(Allahumma rzuqni ḥubbuka, wa ḥubba man yanfa`uni ḥubbuhu `indak. Allahumma ma razaqtani mimma uḥibbu faj’alhu quwwatan li fima tuḥibb. Allahumma wa ma zawaita `anni mimma uḥibbu faj’alhu faraghan li fima tuḥibb). “ (Tirmidhi)
‘Ya Ubangiji ka sada ni da soyayyar ka, da soyayyar sauran mutane da zata amfane ni, Ya Ubangiji ka sanya duk abinda ka azurtani da shi ya zamto zai kafafa mini kusantar ka, Ya Allah duk abinda ka hana ni kuma, Ka mai she shi alkhairi a gare ni.’ Tirmizi ya ruwaito